<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Sahihiyar Ƙauna Dai Ta Fi Kwatanci LW324</title>
<lyrics>[V1]
 1) Sahihiyar ƙauna dai ta fi kwatanci,
 Mun durƙusa a gaban kursiyin,
 Don waɗanda ka haɗa su su sami
 Ƙauna mafificiya a zuciyarsu.

[V2]
 2) Rai mai jamali, kau da shakka duka,
 Tabbatar da ƙauna da bangaskiya,
 Da jurewa da bege da natsuwa,
 Irin da ba ya saurin fushi kuwa.

[V3]
 3) Ba su wadatacciyar murna taka,
 Da kuma kwanciyar rai da kamewa,
 Iyakar kwanakinsu nan a duniya,
 Har ran da za su shiga Sama can.</lyrics>
<hymn_number>324</hymn_number>
</song>